Sama da 'yan Najeriya miliyan 31.8 na fama da matsanancin karancin abinci, lamarin da ya haifar da rashin isasshen abinci mai gina jiki musamman a tsakanin mata da yara ya kara tsananta.
A cewar kididdigar da rahoton kungiyar Cadre Harmonise na 2024 ta fitar, karuwar farashin kayan abinci ya faru ne sakamakon cire tallafin man fetur, tare da kalubalen tsaro, wanda ya jefa miliyoyin 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
A cikin wata sanarwa, Daraktar Sashen Yada Labarai a Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Julie Osagie-Jacobs, ta bayyana cewa abokan huldar kasar, da suka hada da Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), GAIN, GIZ, da Agsys, sun yi wannan bayani a wani taron bita na hadin gwiwa kan aiwatar da tsarin samar da abinci a Najeriya.
Rahoton na Cadre Harmonise na zuwa ne yayin da matsalar ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gona da dama a wasu sassan kasar.
Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya nuna alhininsa ga dubban manoma da lamarin ya shafa.
Wata kididdiga da hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta fitar, ta nuna cewa sama da dubban hektoci na gonaki sun lalace sanadiyyar ambaliyar ruwan, sannan sama da mutum dubu 40 sun rasa muhallansu.
“Wannan zai matukar shafar yawan amfanin gonan da muka yi hasashen za a samu, amma dai muna da kwarin gwiwar hakan ba zai yi matukar tasiri akan abincin da za a girba ba.” In ji Kyari.
“Tabbas, za mu kai ga gaci a hasashen da muka yi na samun isasshen abinci duk da faruwar wannan ibtila’i.” Kyari ya kara da cewa.
Dandalin Mu Tattauna