Shugaban na Najeriya ya yi la’akkari da yadda wannan matsala ta samun kudaden ketare a farashi daban-daban take haifar da cikas ga tattalin arzikin kasa.
Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, masu sayan amfanin gona a kakar bana, na bin manona har gonakinsu suna cinikayyar kayan abinci da manoman suka samar, inda suke biyan duk abin da suka saya kudi a hannu
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana sa ido a kan abubuwa dake faruwa a game da sauyin mallakar katamfaren kamfanin sadarwar zamani, Twitter, biyo bayan sayen kamfanin da sabon shugabansa Elon Musk ya yi.
Wani babban al’amari da har ila yau ya sa kudaden da kamfanin yake kashewa ya karu shi ne, shirin nan na Metaverse da ya tsunduma kansa a ciki, wanda yake cin makudan kudade.
Gabanin nan, mataimakin Ministan ya bayyana yanayin da Nijar take ciki a yau, inda ya ce, a shirye kasar take ta amshi masu zuba hannun jari.
Kasuwar Lafiya-Lamurde da ke karamar hukamar Lamurde a jihar Adamawa kasuwa ce da ke chi mako-mako kuma ita ce kasuwar kayan abinchi da ake alfahari da ita a jihar da ma makwabtanta.
Sama da tan miliyan tara na shinkafa ne ake shigowa da shi a yankin yammacin Afirka, wanda ke lakume kusan dala biliyan 3.4 a cikin lissafin kudin shigowa da kaya a shekarar 2021.
‘Yan siyasar Amurka sun fusata da wannan matsaya da kungiyar ta OPEC ta cin ma, wadda ake ganin za ta kai ga tashin farashin mai.
Tuni dai kamfanonin jiragen sama, wuraren shakatawa, gidajen sayar da abinci da kantunan kayan alatu suka fara wasa wukakensu don tarbar baki.
Shirin Kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya duba irin hobbasar da gwamnatocin jihohi ke yi wajen habbaka harkokin kasuwanci da zasu bada dama wajen kafa kamfanoni don bunkasa tattalin arzikin jihohin da ma kasa baki daya.
Shirin Kasuwa na wannan makon ya leka jihar Neja a Najeriya don tattaunawa da 'yan kasuwa game da farashin kayayyaki da kuma kalubalen da suke fuskanta.
Shirin Kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya ziyarci kasuwar kayan gwari, da ke jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya.
Domin Kari
No media source currently available