A yau Alhamis ne Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana matsayin gwamnati a kan wannan batu a wani taron manema lanbarai a Abuja.
Ministan ya ce rufe dandalin sadarwar a bara ga masu amfani da shi ya biyo bayan yunkurin da wasu bata gari suke yi na haddasa tashin hankali a Najeriya da labaran kanzon kurege da yada bayanan karya da na kiyayya.
Mohammed ya yi gargadi cewa gwamnati bata da niyar hana duk wata kafar sadarwa gudanar da ayyukanta, amma kuma hakan ba zai sa ta kyale a yi amfani da wani dandalin sadarwa a jefa kasar cikin rikici da bala’i.
Ministan ya ce: “Mutane da dama sun yi waya suna tambayarmu ko me zai kasance yarjejeniyar mu da Twitter saboda sauyin mallakarsa.”
“Wasu da dama kuma sun nemi jin martanin mu bayan rahotannin da ke nuna cewa an samu karuwar labaran kanzon kurege, da yada bayanan karya da kuma kalaman nuna kiyayya tun lokacin da shahararren dandalin sadarwa ya sauya ikon mallakarsa.”
Ya kara da cewa, "wasu mutane da yawa ma sun tambaye mu ko zamu sake hana Twitter aiki?.
Ya bayyana cewa, gwamnati tana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Twitter, kuma ko kadan, ba nufinta bane ta haramta duk wani dandalin sada zumunta ba ko kuma murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki.
Bisa ga cewarsa, abin dake faruwa yanzu a shafin Twitter sananne ne ga kowa. Twitter ya zama dandalin zabi ga masu son tada zaune tsaye a Najeriya, ta hanyar yin amfani da labaran karya, da kalaman kiyayya.
Ya kara da cewa, babu wata al’umma da za ta kyale wani dandalin sada zumunta ya jefa ta cikin rudani. Tabbas ba Najeriya ba.