Ku kalli muhawarar farko ta ‘yan takarar shugaban kasa a zaben Amurka tsakanin Joe Biden na jam’iyyar Democrat da Shugaba Donald Trump.
An dai fara muhawarar ce cikin fara’a, wacce ta jirkice ta koma ta musayar kalamai kan batutuwan da aka tattauna akai.
Shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Republic Donald Trump da abokin takararsa na jam’iyyar Democrat tsohon shugaban kasa Joe Biden, sun tafka muhawara a daren jiya Talata.
Amurkawa sama da miliyan 100 ake kyautata zaton za su kalli muhawarar farko tsakanin Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden na Jam'iyyar Demokarat.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Lahadi cewa zai bukaci abokin takararsa na jam’iyar Demokrat a babban zaben uku ga watan Nuwamba, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, da yayi gwajin kwayoyi kafin ko bayan muhawararsu ta ranar Talata.
Shugaban Amurka Donald Trump na ci gaba da bayyana shakkun a kan ingancin zaben kasar na ranar 3 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai gabatar da mace wadda za ta zama Alkali a babbar Kotun Kolin Amurka, biyo bayan mutuwar mai shari’a Ruth Bader Ginsburg.
Makwanni bakwai gabannin gudanar da zabe a Amurka, shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya yi abin a zo a gani wajen yaki da annobar coronavirus da kuma dakile yawan mace-mace a kasar.
Yayainda Amurka da Manyan kasashen duniya ke rige-rigen samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 don kawar da annobar a doran kasa, al'amarin ya zama abin sukar juna tsakanin yan takarar shugabancin Amurka gabanin zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba.
Jami’an leken asirin Amurka sun daina yi wa majalisar dokoki bayani akan sha’anin tsaro ga zaben kasar, lamarin da ya janyo kakkausan martani daga ‘yan jam’iyyar adawa ta Demokrats.
Donald J. Trump, shugaban kasar Amurka na 45, kuma shugaba na 3 da aka tsige shi amma kuma ya sami kubuta, yana neman sake zabensa a wa’adin mulki na 2 a watan Nuwamba.
Domin Kari
No media source currently available