Hukumomi a Kenya sun saka dokar hana fita a unguwar Eastleigh da ‘yan kasar Somalia keda tarin yawa a birnin Nairobi, saboda yawan kamuwa da coronavirus.
A wannan mako a jihar Michigan, masu zanga zanga sun taru gaban Majalisar jihar domin bayyana damuwarsu ga dokokin hana zirga zirga.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.