Wani Jami’in kiwon lafiya a Amurka da a lokacin kwarmata bayanai ya yi zargin an cire shi daga mukaminsa saboda ba da muhimmaci kan kimiyya a kwamitin da gwamanti ta kafa na yaki da cutar coronavirus, ya shirya tsaf domin fadawa ‘yan majalisar dokoki yau Alhamis cewa dole a gayawa jama’a gaskiya kana kar a bada labarin da aka tace shi saboda dalilai na siyasa.
“Dole mu sani kuma mu fahimci abinda muka tunkara. Muna da masana kimiyya da suka shahara a duniya, dole ne a basu dama su yi jagoranci, “Dr. Rick Bright ya fada a sakonsa na bayanin da zai bude zaman, wanda aka wallafa kafin a fara zaman sauraran bahasin na karamin kwamitin Lafiya na Majalisar dokokin.
‘Yan majalisar na son su sami karin bayanai a kan matakan da gwamnatin tarraya ta ke dauka game da annobar, wadda ta kashe sama da mutum dubu 84,000 a Amurka.
Bright ya fada cewa, ya fara gargadin shugabannin ma’aikatar lafiya da walwalar al’umma a tun a watan Janairu kan karanci kayan kariya, da jami’an lafiya a Amurka suke bukata domin su kula da marsa lafiyar da suka kamu da COVID-19.
Facebook Forum