Kungiyar jaruman fina-finan Hollywood ta cimma matsaya da kamfanonin hada fina-finai a ranar Laraba don kawo karshen yajin aikin da ta yi, wanda ya kawo kusan watanni na rikicin ma’aikata ya kuma kawo cikas ga masana’antar nishadi a tarihi.
Jama’a da dama kan zargin ‘yan TikTok da bata tarbiyyar matasa duba da irin hotunan bidiyo da suke yadawa a shafin na sada zumunta mai mabiya biliyan daya a duniya.
Jazimine Okafor, diyar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood John Okafor, wanda aka fi sani da Mr. Ibu ce ta tabbatar da cewa an yanke kafar mahaifinta.
Lionel Messi na kasar Argentina ne ya lashe kambun na bana yayin da ya kara da zaratan ‘yan wasa irinsu Erling Haaland.
“A gaskiya wadannan maganganu da suka fita daga bakin mawakin ya sa na ga cewa tsayawa a ba shi amsa a matakin hankali ma bata lokaci ne." In ji Ahmad.
Ana sa ran mawakan biyu da aka gayyata za su bayyana ne a gaban kwamitin majalisar a ranar Talata mai zuwa.
Wannan wata alama ce da ke nuni da bunkasa da masana’antar fina-finan ta Najeriya da ake kira Nollywood ke yi a cewar kwararru a fannin shirya fina-finai.
A wannan makon fitacciyar jarumar ta fasa kwan cewa ita da Will sun rabu tun a shekarar 2016, amma ba su fadawa duniya ba.
Madonna mai shekaru 65, ta yi fitattatun wakokinta da ta yi cikin shekaru 40 da ta kwashe a fannin nishadantarwa.
'Yan sandan Sun tsare Azeez Fashola ne wanda aka fi sani da Naira Marley bisa tuhumar da ake masa da hannu a mutuwar Mohbad wani mawaki da yake karkashin wanda ake zargin kafin mutuwarshi.
Naira Marley da Sam Larry sun sha musanta hannu a mutuwar MohBad, wanda ya rasu cikin wani yanayi mai sarkakiya.
Jama’a da dama na ta dora alhakin mutuwar Mohbad akan Naira Marley wanda shi ne tsohon maigidansa da ya fara daukansa a aiki a kamfaninsa na Marlians. Naira Marley ya musanta zargin.
Domin Kari
No media source currently available
Ya Fitattun Mutane Ke Amfani Da Kafofin Sadarwa?