Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madonna Ta Kaddamar Da Rangadin Wasanninta A London


Madonna
Madonna

Madonna mai shekaru 65, ta yi fitattatun wakokinta da ta yi cikin shekaru 40 da ta kwashe a fannin nishadantarwa.

Fitacciyar mawaki Madonna ta kaddamar da zangon wasanninta a babban zauren 02 da ke birnin London.

Wasan wanda somin-tabin wasannin da za ta yi ne, ya gudana ne a ranar Asabar.

Shi ne kuma wasa na farko da ta yi tun bayan da harbu da kwayar bacteria da ta saka mata mummunar rashin lafiya.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na AP Sian Watson ya kwatanta wasan na London a matsayin wani gagarumin biki.

Madonna mai shekaru 65, ta yi fitattatun wakokinta da ta yi cikin shekaru 40 da ta kwashe a fannin nishadantarwa inda ta burge masoyanta.

“Ban yi tsammanin zan yi rai ba.” In ji Madonna a lokacin da take magana kan rashin lafiyarta a wurin wasan

Ta kara da cewa, ‘ya’yanta ne suka ba ta kwarin gwiwar ta tsaya tsayin daka wajen yakar cutar.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG