Masana na ganin shugabanin biyu zasu tattauna akan abubuwa da yawa saboda Amurka na son kasancewa kan gaba cikin kasashen dake taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci, sai dai akwai bukatar Najeriya din ta yi taka tsantsan da wasu halayen kasashen yammacin Turai
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari na shirin ganawa da shugaban Amurka Donald Trump gobe Litinin a birnin Washington DC.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kan hanyarsa ta zuwa Amurka domin amsa gayyatar takwaransa shugaba Donald Trump.
Ranar Asabar idan Allah ya kaimu shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai amsa goron gayyatar shugaban Amurka Donald Trump, inda zai kai wata gajeriyar ziyarar aiki.
Wannan ziyarar aiki da shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai kawo Amurka makon gobe ta biyo bayan gayyatar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi masa ne kuma ana ganin zasu tattauna akan abubuwa da dama da suka hada da harkokin tsaro da yaki da cin hanci da rashawa