Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nazarin Ziyarar Da Shugaban Najeriya Zai Kawo Nan Amurka


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Wannan ziyarar aiki da shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai kawo Amurka makon gobe ta biyo bayan gayyatar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi masa ne kuma ana ganin zasu tattauna akan abubuwa da dama da suka hada da harkokin tsaro da yaki da cin hanci da rashawa

Bisa ga gayyatar Shugaban Amurka Donald Trump,Shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai fara ziyarar aiki a nan Amurka daga ranar 29 ga wannan watan.

Ana kyautata zato a ganawar shugabannin biyu zasu tattauna alamuran tsaro da cinikayya da dai wasu abubuwa makamantansu, musamman matakan da ita Amurka zata dauka wajen taimakawa Najeriya da yaki da ta’addanci da kuma cin hanci da rashawa.

Dr. Usman Muhammad wani mai sharhi akan alamuran diflomasiya da sha’anin kasa da kasa ya yi tsokaci akan abubuwan da yake gani zasu yi tasiri a wannan ganawar ta shugabannin.

A ganin Dr Usman akwai batun yaki da shugaba Buhari ya keyi da cin hanci da rashawa. Ya ce akwai kudade da yawa da Amurka ta kwace daga wasu da suka hada da tsohuwar minister man fetur wadda take da kudade da gidaje a wasu jihohin Amurka. Za’a yi maganar ta da wasu barayin da suka boye kudade a kasar Amurka.

Baicin hakan akwai bayanan sirri da Shugaba Buhari bai sani ba da za’a shaida masa.

Abu na biyu shi ne maganar yaki da Boko Haram da yawan tashin hankali dake aukuwa a wurare daban daban cikin kasar, musamman kashe-kashen da a keyi a jihar Binuwai tsakanin makiyaya da manoma. Amurka zata bayyana irin taimakon da zata ba Najeriya.

Dr Usman yace gwamnatin Amurka na iya ba Shugaba Buhari bayanai akan wasu mukarrabansa da suke da hannu dumu-dumu cikin cin hanci da rashawa a Najeriya.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG