Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ganawar Shugaba Buhari Da Trump Za Ta Haifar?


Buhari (Hagu) Trump (Dama)
Buhari (Hagu) Trump (Dama)

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari na shirin ganawa da shugaban Amurka Donald Trump gobe Litinin a birnin Washington DC.

Shugaba Buhari zai kasance na farko a nahiyar Afirka da ya fara samun goron gayyata daga gwamnatin Donald Trump.

Dangantakar Amurka da kasashen Afirka ta samu koma baya a watan Maris, lokacin da Trump ya kori tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, yayin da yake Najeriya a wata ziyarar farko da ya kai kasashen Afirka.

A wata sanarwa da Fadar White House ta fitar, ta ce tattaunawar da shugabannin biyu za su yi gobe Litinin za ta mayar da hankali ne kan yaki da ta’addanci da samar da zaman lafiya da kuma hanyoyin da kasashen biyu za su karfafa dangantakar da take tsakaninsu.

‘Yan Najeriya na fadin albarkacin bakinsu game da wannan ganawa da shugabanin biyu za su yi, inda wasu ke ganin Amurka za ta iya taka rawa wajen taimakawa Najeriya ta magance matsalolin tsaron da take fama da su, da suka hada da Boko Haram da kuma rikicin makiyaya da manoma.

Takaddamar Sayen Makamai a Lokacin Mulkin Obama

A baya Najeriya ta nemi Amurka ta sayar mata da jiragen yaki domin kawo karshen masu tayar da kayar baya a arewa maso gabashin kasar, amma tsohon shugaban kasar Barack Obama ya dakatar da yarjejeniyar cinikin jiragen.

Amurka ta dauki matakin ne bayan wani harin da wani jirgin saman yakin Najeriya ya kai kan sansanin ‘yan gudun hijira da ke kusa da iyakar Nigeria da kasar Kamaru bisa kuskure.

Akalla mutane 230 rahotanni suka ce sun rasu sanadiyar harin wanda dakarun Najeriya sun ce harin ya kaikaici mayakan Boko Haram ne.

Bayan da shugaba Donald Trump ya hau mulki ya buga wa shugaba Mohammadu Buhari na Nigeriaya waya, inda ya sanar da shi cewa ya goyi bayan sayarwa da Najeriya jiragen yakin domin ta yaki ta’addanci.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG