A jiya laraba Amurka ta dorawa wasu mutane 3 da kamfanoni 4 takunkumi a sassan kasashen Iran, da hadaddiyar daular larabawa da Turkiyya, bisa dalilin zargin su da taimakawa wajen fitar da kayayyaki, da sayen fasahohi daga kamfanonin Amurka zuwa kasar Iran da babban bankin kasar.