Walz, wanda Gwamna ne mai ci kuma tsohon soja, ya taka muhimmiyar rawa wajen kare ‘yancin zubar da ciki a Amurka.
Kasuwannin hannayen jari a fadin duniya na tangal tangal, yayin da ake fargabar tsunduma cikin matsalar tsananin tsadar kaya musamman ma a manyan kasashe irin Amurka da Japan da sauransu
Shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada cewa fito da Amurkawa da sauran ‘yan wasu kasashen daga gidajen yarin Rasha wata babbar nasarace ta bangaren diflomasiyya da kawance.
Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka ta fada a ranar Talata cewa, tana shirin kashe dala miliyan 10 don dakile kamuwa da cutar murar tsuntsaye tsakanin ma’aikatan gona, da ya hada da dala miliyan 5 don rigakafin mura na lokaci-lokaci.
Akalla yara ‘yan asalin Amurka 973 ne suka mutu a tsarin makarantun kwana na gwamnatin Amurka inda ake cin zarafin yaran, bisa ga sakamakon wani bincike da jami’ai suka fitar jiya talata da suka yi kira ga gwamnati da ta sa makarantun sun nemi afuwar daliban.
Amurka da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan kasashensu mazauna a Najeriya, kan su zauna cikin shiri kan yiwuwar barkewar rikici yayin zanga-zangar da aka shirya za a yi a kasar.
Ta yiwu abokan hamayya a zaben Amurka da ke tafe, mataimakiyar shugaban kasar Kamala Harris da tsohon shugaba Donald Trump sun bayyana mabambantan ra'ayoyi game da yadda Isra'ila ke yin yaki a Gaza, a lokacin da suka gana da Firai Minista Benjamin Netanyahu a lokuta dabam dabam a wannan makon.
A yau Juma’a, tsohon shugaban Amurka Barack Obama da mai dakinsa Michelle sun bayyana goyon bayansu ga Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris a matsayin wacce za ta yi wa jam’iyyar Democrat takarar shugaban kasa.
Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ke kare yakin da kasar ke yi a Gaza, a yayin jawabi da ya yi a zauren Majalisar dokokin Amurka.
Shugaba Joe Biden ya janye daga takarar ci gaba da zama a fadar White House sannan a maimakon hakan ya bayyana goyon bayansa ga mataimakiyarsa, Kamala Harris.
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai samu tarba daga ‘yan Majalisar Dokokin Amurka dake fama da mummunan rabuwar kai da al’ummar kasar da suka shagaltu da wasu al’amura da kuma gagarumin gangamin zanga-zanga a yau Laraba yayin gabatar da jawabi gaban majalisar a karo na 4 a tarihi
Daraktar hukumar leken asiri ta Amurka, Kimberly Cheatle ta yi murabus daga aikinta, a cewar sakon imel da ta aike wa ma'aikatanta a yau Talata
Domin Kari