Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Kananan Yara 'Yan Asalin Amurka 1,000 Suka Mutu A Makarantun Kwana


Makarantar kwana na yaran 'yan asalin Amurka
Makarantar kwana na yaran 'yan asalin Amurka

Akalla yara ‘yan asalin Amurka 973 ne suka mutu a tsarin makarantun kwana na gwamnatin Amurka inda ake cin zarafin yaran, bisa ga sakamakon wani bincike da jami’ai suka fitar jiya talata da suka yi kira ga gwamnati da ta sa makarantun sun nemi afuwar daliban.

Binciken da sakataren harkokin cikin gida Deb Haaland ta kaddamar ya gano kaburbura 65 daga cikin fiye da 400 na yaran da suka mutu a makarantun kwana na Amurka da aka kafa domin tilasta wa yara 'yan asalin Amurka zama fararen fata. Sakamakon binciken bai fayyace yadda kowane yaro ya mutu ba, amma abubuwan da suka haddasa mutuwar sun hada da rashin lafiya, hadurra da kuma cin zarafi a cikin shekaru 150 da aka yi ana gudanar da makarantun da ya kawo karshe a 1969, in ji jami'ai.

Sakamakon binciken ya biyo bayan zaman sauraren da aka yi a fadin Amurka cikin shekaru biyu da suka gabata, inda dimbin tsoffin daliban suka bayyana irin bakar wahala da suka sha da kuma yawan wulakanci da suka sha yayin rabuwa da iyalansu.

Shaidar kabarin wadanda su ka mutu a makarantar kwana ta yara 'yan asalin Amurka
Shaidar kabarin wadanda su ka mutu a makarantar kwana ta yara 'yan asalin Amurka

A wani rahoto na farko da aka fitar a shekarar 2022, jami’ai sun kiyasta cewa, sama da yara 500 ne suka mutu a makarantun. Gwamnatin tarayya ta zartar da dokoki da manufofi a shekarar 1819 don tallafawa makarantun, da aka ci gaba da aiwatarwa har cikin shekarar 1960.

Makarantun sun ba yara 'yan asalin Amurka sunayen Ingilishi, suna sanya su a cikin atisayen soji tare da tilasta musu yin aikin hannu, kamar noma, yin bulo da aikin jirgin kasa, in ji jami'ai.

Dattawan 'yan asalin Amurka suna sauraron masu gabatar da bahasi
Dattawan 'yan asalin Amurka suna sauraron masu gabatar da bahasi

Tsofaffin dalibai sun ba da labarin irin akuba da aka gasa masu suna hawaye yayin zaman sauraren bahasi a Oklahoma, South Dakota, Michigan, Arizona, Alaska da sauran jihohi. Sun yi magana game da azabtar da su saboda suna magana da yarensu, an kulle su a dakunan karkashin gidaje, da kuma aske masu gashin kansu don badda asalinsu. Wani lokaci ana kulle su a wadansu dakuna su kadai, ana yi masu duka da hana su abinci. Da yawa daga cikinsu sun bar makarantun ba su da wani ilimi ko kwarewar sana'ar da za su iya yin wani kirki ba.

Sabon rahoton bai fayyace wanda ya kamata ya nemi ahuwar a madadin gwamnatin tarayya ba, yana mai cewa, ya kamata a fitar da shi ta hanyar da ta dace da kuma jami'ai da suka dace don nuna cewa an yi shi ne a madadin jama'ar Amurka kuma a biyo bayanshi da tsare-tsare masu karfi da za a aiwatar."

Wani yana bayyana akuba da ya sha a makarantar 'yan asalin Amurka s
Wani yana bayyana akuba da ya sha a makarantar 'yan asalin Amurka s

Jami'an Ma'aikatar Cikin Gida sun kuma ba da shawarar cewa, gwamnati ta saka hannun jari a shirye-shiryen da za su taimaka wa al'ummomin Amurkawa su warke daga raunin da makarantun kwana ke haifarwa. Wannan ya hada da kudi don ilimi, shawo kan tashin hankali, da farfado da harsunan asali. Kamata ya yi kudin da za a kashe kan wadannan kokarin ya yi daidai da kudin da aka kashe a makarantun, in ji jami’an hukumar.

Makarantun, cibiyoyi makamantansu, da shirye-shirye masu alaka sun sami tallafin sama da dala biliyan 23 a a tsarin kashe kudin da gwamnatin tarayya idan aka kwatanta da tsadar rayuwa a yau, in ji jami'ai.

A shekara ta 1926, fiye da kashi 80 cikin 100 na yaran da suka kai shekarun makaranta - yara 60,000 - suna halartar makarantun kwana wadanda gwamnatin tarayya ko kungiyoyin addini ke gudanarwa, a cewar kungiyar ‘yan asalin Amurka ta kasa da ke kokarin sanyaya ran wadanda wannan tsarin ya shafa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG