Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Musayar Fursunoni Tsakanin Amurka Da Rasha


US President Joe Biden and Vice President Kamala Harris watch as former prisoner held by Russia US-Russian journalist Alsu Kurmasheva embraces her family as she arrives at Joint Base Andrews in Maryland on August 1, 2024.
US President Joe Biden and Vice President Kamala Harris watch as former prisoner held by Russia US-Russian journalist Alsu Kurmasheva embraces her family as she arrives at Joint Base Andrews in Maryland on August 1, 2024.

Shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada cewa fito da Amurkawa da sauran ‘yan wasu kasashen daga gidajen yarin Rasha wata babbar nasarace ta bangaren diflomasiyya da kawance.

Musayar fursunoni da aka yi jiya Alhamis tsakanin Rasha da kasashen Yammacin duniya ya samo asali ne lokaci mai tsawo da ke cike da sarkakiya, wanda kuma aka kwashe dogon lokaci ana tattaunawar diflomasiyya tsakanin kasashe.

Shugaban Amurka Joe Biden, a cikin jawabin da ya yi daga fadar White House, tare da 'yan uwan Amurkawan da aka 'yantar, ya jaddada yadda Amurka ta yi aiki kafada-da-kafada da manyan kasashe abokan huldarta a Turai.

Shugaban Amurka Joe Biden, Tare Da 'Yan Uwan Fursunonin Da Ke Tsare A Rasha Da Aka Sako
Shugaban Amurka Joe Biden, Tare Da 'Yan Uwan Fursunonin Da Ke Tsare A Rasha Da Aka Sako

Biden ya jaddada cewa fito da Amurkawa da sauran ‘yan wasu kasashe daga gidajen yarin Rasha wata babbar nasarace ta bangaren diflomasiyya da kawance.

Yace, "Don haka ga duk wanda ke tambaya ko abokan kwance na da mahimmanci, lallai haka ne. Suna da mahimmanci."

Amurkawan Da Aka Sako Daga Rasha
Amurkawan Da Aka Sako Daga Rasha

Jawabin na shugaban kasar na jam'iyyar Democrat inda ya jaddada muhimancin kawance, ya bambanta da na tsohon shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Donald Trump, wanda harkokin cikin gida ne ya fi maida hankali akai.

An tambayi Biden kan abinda zai ce game da ikirarin Trump na cewa zai iya 'yantar da dukkan Amurkawa ba tare da wata yarjejeniya ba.

Biden ya amsa da cewa, "Me yasa bai yi haka ba a lokacin da yake shugaban kasa?"

Daga bisani Trump, ya caccaki yarjejeniyar a shafukan sada zumunta, inda ya kira musayar fursunonin a matsayin barazana ga Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG