Wannan shi ne na baya-bayan nan na abin da ofishin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana da "Hare-hare kan makarantu a wayance" na Isra'ila, tare da a kalla hare-hare 21, tun daga ranar 4 ga watan Yuli, inda kuma suka hallaka daruruwan mutane, ciki har da mata da kananan yara.