Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Ta Yiwu Akwai Teku a Karkashin Duniyar Mars


Hoton Duniyar Mars
Hoton Duniyar Mars

A ci gaba da gano abubuwan al'ajibi da masu ilimin kimiyya ke yi, sun gano cewa ga dukkan alamu akwai dinbin ruwa karkashin duniyar Mars.

Da alamar akwai wani babban teku a wuri mai nisan kilomita 10 zuwa 20 kasa da doron duniyar Mars, a cewar wani binciken da aka wallafa a ranar Litini a mujallar Proceedings of the National Academy of Sciences.

Masana ilimin kimiyya sun ce akwai yiwuwar samun isasshen ruwa a duniyar ta Mars wanda zai iya kai munzalin teku a duniyar ta mars wadda ake wa lakabi da jar duniya.

Sakamakon binciken ya fito ne daga shekaru hudu na bayanai da aka tattara daga mujallar NASA’s Mars InSight lander daga shekara ta 2018 zuwa 2022. Wannan lander din (wato jirgi mai sauko duniyar Mars) na da na’urar sunsuno abubuwan karkashin kasa ta seismometer a cikin kayan aikinsa wanda ya yi amfani da su wajen nadar girgizar duniyar Mars (marsquakes) sau 1,300 kafin ya Adaina nadar girgizar duniyar ta Mars.

Masu bincike, wadanda har yanzu suke nazarin bayanan, sun samu damar amfani da bayanan girgizar kasa don tantance irin kayan da girgizar ke haduwa da su yayin faruwarta.

Farfesa Michael Manga na Jami’ar California, Berkeley, wanda ke cikin tawagar binciken, ya gaya wa BBC cewa masana kimiyya sun yi amfani da wadannan fasahohin a binciken Mars da suke amfani da su a Duniya don nemo ruwa.

Masana kimiyya sun ce duniyar Mars ta kasance da isasshen ruwa a samanta miliyoyin a shekaru da suka gabata a matsayin nau'ukan koguna, tabkuna da watakila ma teku.

Masu bincike na kyautata zaton cewa yayin da sararin saman duniyar ta Mars ya matse, wasu daga cikin ruwansa sun yoye kasa yayin da sauran ruwan ya salwance a sararin sama, wanda ya sa Mars ta zama hamada kimanin shekaru biliyan 3 da suka gabata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG