“Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowane ‘dan takara a zaben Najeriya. Ta ce ita dai babban muradinta shi ne ta ga an gudanar da ingantaccen zabe, na gaskiya mai cike da adalci, wanda kowa da kowa zai na'am da shi”
Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a jiya Talata cewa, labarin Amurka labari ne na ci gaba da jajircewa, yayin da yake jawabi a kan halin da kasa ke ciki da ya maida hankali a kan manufofin tattalin arzikin na cikin gida, inda ya kara da kira ga ‘yan adawa na Republican da su hadu su yi aiki tare.
Sojojin Amurka sun ce sun kakkabo wannan baban bala-balan din kasar China na leken asiri a yankin gabar tekun Carolina.
A wani mataki na nuna goyon baya ga tsarin dimokaradiyya a Naijerya, Amurka ta sanya takunkumin bulaguro ga mutanen da ke da hannu wajen yin zagon kasa ga dimokradiyya a Najeriya
An zabi Temilade Openiyi, wacce aka fi sani da Tems, a jerin sunayen fitattun ‘yan wasan fina finai na lambar Yabo ta Oscars 2023, saboda gudunmawar da ta bayar a rubuta wakar da ake kira ‘Lift Me Up’, daya daga cikin wakokin sauti na wani fitaccen silma na Marvel’ Black Panther: Wakanda Forever.
Wani mutum ya harbe mutane 10 a wani wurin shagalin bikin murnar sabuwar shekara ta kasar China a wani birni da ke gabashin birnin Los Angeles, kuma har yanzu ana nemansa ruwa a jallo a cewar ‘yan sanda.
Lisa Marie Presley, mawakiya kuma diya daya tilo ga fitaccen mawakin nan Elvis Presley, ta rasu jiya Alhamis bayan da aka garzaya da ita wani asibiti a yankin Los Angeles, kamar yadda mahaifiyarta ta bayyana.
Bayan wata mahaukaciyar guguwar da ta yi kaca-kaca da wasu yankunan California a Amurka, ana ta yunkurin shara tare da gyara barnar da ta yi a ranar Laraba, yayin da aka samu saukin saukar ruwan sama a yankuna da dama.
Kwamitin bincike na musamman a jihar Geogia ta Amurka, da ke binciken ko shugaban kasar na wancan lokacin Donald Trump da abokansa sun aikata wani laifi yayin da suke kokarin juya zaben da ya fadi a shekarar 2020 ya kammala aikinsa.
Bayan kwashe zagaye 15 ana kada kuri'a cikin kwanaki biyar ga dan jam'iyyar Republican mai sausaucin ra’ayi, daga karshe an zabi Kevin McCarthy a matsayin kakakin majalisar wakilan Amurka a yau Asabar.
Wannan dai shi ne karon farko cikin shakaru 100 da wanda ake ganin zai zama kakakin majalisar wakilai ya gaza lashe zaben kujerar a zagayen farko.
Kamfanin Twitter ya dakatar da hada dandalin da manyan shafuka irinsu Facebook da Instagram, da abokan hamayyarsa Mastodan, Tribel, Nostr, Post, da Truth Social na tsohon shugaban kasa Donald Trump.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.