Najeriya ta bukaci Google da ta kawo karshen amfani da kafar YouTube da kafofi na kai tsaye da haramtattun kungiyoyi da kungiyoyin 'yan ta'adda ke yi a kasar, in ji ministan yada labarai Lai Mohammed.
Kafin kotun ta yanke hukunci, tauraruwar kwallon kwandon ta Amurka Brittney Griner ta nemi afuwar 'yan uwanta da tawagarta yayin da ta saurari shari'ar da ake yi mata ta mallakar miyagun kwayoyi.
Tun bayan sanarwar da Amurka ta bayar jiya na kashe shugaban kungiyar Al-Qaeda, Ayman al-Zawahiri a Kabul, masu sharhi ke ci gaba da tsokaci a game da muhimmancin kisan ga fafutukar yaki da ta’addanci a duniya da kuma Amurka.
Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa, an kashe shugaban kungiyar Al Qaeda Ayman al-Zawahiri a wani harin da hukumar leken asiri ta CIA ta kai a Afganistan a karshen mako, wanda shi ne tashin hankali mafi girma ga kungiyar tun bayan kashe wanda ya kafa kungiyar Osama bin Laden a shekarar 2011.
Ivana Trump, tsohuwar matar tsohon shugaban Amurka Donald Trump ta farko, kuma mahaifiyar ‘ya’yan shi uku na farko ta rasu tana da shekaru 73 a duniya.
Da ma dai an jima ana tsammanin wannan matsaya da kotun ta dauka ta soke dokar da ta ba mata damar zubar da ciki wacce aka kwashe shekaru 50 ana amfani da ita
Jami’an kiwon lafiya a Amurka sun fada jiya Laraba cewa, kusan 1 cikin 5 na Amurkawa manya da suka bada rahoton kamuwa da cutar COVID-19 a baya, har yanzu suna fama da alamomin COVID din na dogon lokaci, bisa ga bayanan bincike da aka tattara a cikin makonnin biyun farkon watan Yuni da ya gabata.
Farashin man fetur ya haifar da kaso mafi girma na hauhawar farashin kayayyakin masarufi, hayar gidaje, farashin tikitin hawa jiragen sama da sauran abubuwa da dama.
Rundunar Mayakan Amurka ta Horas da manyan kwamandojin sojojin Najeriyar da nufin lalubo karin hanyoyin da za ake kare fararen hular da ba suji ba basu gani ba yayin da sojoji ke fafatawa ko kuma wani aikin samar da zaman lafiya a sassan Najeriya.
Majiyoyi sun ce Biden na shirin tafiya Saudiyya, tare da tafiya Turai da ma Isra'ila a karshen watan Yuni.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa dan bindigar ya harbe kansa bayan da ya kashe mutanen.
An ware ranar ce don karfafa muhimmanci kula da tsaftar jiki a lokacin da mace ke al’ada da kuma wayar da kan jama’a.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.