Gasar ta 2017 ta hada da kungiyoyi daga kasashen Gabon, Guinea-Bissau, Aljeriya, Zimbabwe, Cote D'Ivoire, Togo, Burkina Faso, Kamaru, Tunisiya, Senegal, Kwango-Kinshasa da kuma Morocco.
Gasar Cin Kofin Afirka ta 2017 da za a yi a kasar Gabon, ita ce ta 31 tun da aka fara wannan gasa tsakanin kasashen Afirka. Gasar, wadda ake kira AFCON a takaice, Hukumar Kwallon kafa ta Afirka ce ke shiryawa don kungiyoyin kwallon kafa na maza na Afirka.