Iyayen ‘yan matan da ‘yan bindiga suka sace a makaranta sun gayawa gwamna ranar litinin cewa sunje neman su a cikin daji,sun kara da cewa har yanzu ba’a ga ‘yan mata dari biyu da talatin da hudu ba,fiye da adadin da gwamnati ta bada. An dauki hotuna 22 Afrilu 2014.
Iyayen dalibai mata fiye da dari biyu da ‘yan bindiga suka sace a makaranta a garin Chibok har yanzu ba’a gansu ba bayan mako daya,duk da kokarin da jami’an tsaro da wasu iyayen yaran suka yi na binsu cikin mugun daji.Wasu daga cikin daliban su tsira da tsalle daga mota ko kuma boyewa a cikin daji.