'Yar majalisar dattawan Amurka Frederica Wilson 'yar jam'iyar Democrats ta Amurka kuma 'yar gwagwarmayar ganin an dawo da 'yan matan cibok.
Larabannan ne masu fafutukar gani an ceto daliban Chibok suka kai ziyara fadar shugaban Najeriya inda suka gana Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari Ya Gana da Masu Hankoron Ganin An Sako 'Yan Matan Chibok
Albarkacin cikon shekara daya da sace 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka yi a arewacin Najeriya, Muryar Amurka za ta shirya wata muhawara tsakanin kwararrun masanan da za su tattauna batun sace 'yan matan, da kuma kalubalen kubutar da 'yan matan dake hannun 'yan Boko Haram har yanzu.
Ba Mu Manta Da 'Yan Matan Chibok Ba
A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar boko haram ne, suka shiga wata makarantar sakandare a garin Chibok dake jihar Borno suka sace wasu ‘yan mata guda 276.
Masu zanga-zangar lumana sunyi kira ga Gwamnati da ta ceto ;yan matan da aka sace daga makaranta ya'u shekara daya kennan, a Abuja Najeriya, Litinin 13, ga Afirilu 2015. Kusan 'yan mata dari uku ne aka sace wasu daga cikin sun samu sun kubuta da kansu.
Domin Kari