Wadannan kananan hafsoshi sun samu horaswa a wani bangare na koyon aikin soja a makarantar NDA dake Kaduna.
Jigogin na jam’iyyar PDP sun yi tattaki zuwa Sokoto domin karbar tsohon gwamna Attahiru Bafarawa wanda ya canja sheka daga jam'iyyar APC
Magoya bayan jam’iyyun dake mulki daga duk fadin Nijar sun hallara a Yamai a wani gangamin da aka bayyana a zaman tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC mai kula da Arewa maso Gabas, Dr. Umar Duhu, yace kalamun ministan neman haddasa fitina a cikin kasa ce.
Kungiyoyi 7 karkashin jam'iyyar NCP sun yi gangamin nuna rashin jin dadin rashin wutar lantarki a Najeriya
A wani mummunan hadarin mota a jihar Taraba akalla mutane goma sha uku suka rasa rayukansu yawancinsu konewa suka yi sabili da man fetur.
Rundunar tsaro ta Special Tax Force a jihar Flato, ta tabbatar da mutuwar mutane goma sha hudu, da suka hada da jami’an tsaro biyu a wani rikicin da ya auku a wasu kauyuka dake karamar hukumar Riyom, a jihar Flato.
Senata Mamman Magoro, shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Dattijan Nigeria, yace harkar tsaro ta shafi kowa.
Yunkurin da kungiyar dattawan arewa ke yi na gurfanar da Janaral Ihejirika gaban kotun kasa da kasa bisa ga zargin cin zarafin 'yan Najeriya musamman a arewa maso gabashin kasar ya samu goyon bayan kungiyoyin matasan arewa masu zaman kansu.
Maimartaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai Umar El-Kanemi ya yi alawadai da hare-haren da 'yanbindiga sukan kai kan kauyukan Borno da ma kauyukan jihar Adamawa
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janaral Mohammed Buhari ya ce neman sulhu da Boko Haram shi ne kadai zai kaiga samun zaman lafiya a kasar.
Yawan hare haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa kan kauyuka ya sa daruruwan mutane a wasu kauyukan jihar Adamawa suna gudu zuwa wasu wuraren.
Domin Kari