Yace “sha’anin tsaro ya shafi kowa da kowa. Kuma kowa na da irin rawar da zai taka a ciki. Kai dake can baka da bindiga, idan kaga abu wanda kake tuhuma, wanda yake ba dai-dai bane, ka dauki waya buga akwai lambobin jami’an tsaro. Ka fadakar da su, ga kai abunda kake ta gani, ga kuma tuhumar da kake da shi.”
Sahabo Aliyu na Muryar Amurka ya tambaye shi ko me za’ayi domin kyautata hulda tsakanin jami’an tsaro da jama’a, saboda fargaba da jama’a suke da shi na kiran jami’an tsaro idan suka ga wani abu ba dai-dai ba?
Senata Magoro yace “wannan tsoro ai yana zuwa ne idan sai mutum yaje Caji ofis na ‘yan sanda yace nine wane, ga abunda na gani a wuri kaza. Yanzu an riga an wuce wannan. Akwai lambobi, zaka iya kira ba sai an ganka ba. Ba ma sai ka bada sunnanka ba. Abunda muke fata shine karbar sahihan bayanai, kar a bata lokaci a duba lamarin a ga babu komai. Abunda ake gudu kennan."