Kaftin Salisu yace “ranar talatin da daya ga watan Junairu, a wasu kauyukan jihar Kaduna, akwai wani hari da aka kai, inda aka kashe shanu kimanin arba’in, da kuma awaki kamar talatin. Wurin bakin iyaka ne tsakanin jihar Flato da Kaduna.”
“Abkuwar wannan abu yasa mun kula da mutanen Fulani da yawa da suke shigowa jihar Flato. Bayan haka Komandojin wannan yanki sun hadu da sarkin Ganawurin akan cewa ya kira tattaunawa da kungiyoyin da suke wajen saboda da samun zaman lafiya” a cewar Kaftin Salisu.
Amma a wannan rana, ‘yan bindiga sun kara kai wani hari.
Kaftin Salisu yayi karin bayani “Ranar kuma, misalin karfe biyar da rabi, bayan aukuwar wannan meeting din nasu kennan, sai muka samu labarin cewa an kai hari a wani kauye da ake kira Zadiyom wanda yake karkashin Ganawuri a karamar hukumar Riyom. Maharan sun kashe kamar mutane goma sha hudu a wajen, mata shida, maza shida, da yara guda biyu. Sannan sun kashe jami’an tsaro guda biyu, da Sojan Ruwa, da dan sandan ababen hawa, wato Mopol. Sun kuma kona gidaje kimanin ashirin da daya, da majami’a, da mashina kamar guda biyar. Abkuwar wannan abu yasa an saka jami’an tsaro a wajen domin a samu zaman lafiya.”
“Yayin da wannan abu yake faruwa, wasu garuruwan da suka ji abunda yake faruwa a wannan kauye, saboda ana tsammani Fulani ne suka kai wannan hari, sai suka fara kona gidajen Fulani da suke waddannan kauyukan. To munyi kokari mun je mun hana su.”