Shuwagaban majalisar dattawan Najeriya David Mark, da kakakin majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal sun gana da gungun mata masu zanga-zangar lumana na neman hukumomi su dauki mataki domin ceto mata dalibai wadanda ‘yan bindiga suka sace a makarantar Sakandare dake Cibok sama da makonni biyu kennan.
Gwamnatin Jihar Neja ta kafa kwamitin bincike akan wasu masu tsattsauran ra'ayin addini da suka bullo a garin Bida cikin Jihar Neja.
Shugabannin fulani a Nigeria sunce har yanzu babu wani bayani daga gwmnatin kasar akan Fulanin nan da sojojin Nigeria suka yima kisan gilla a jihar Nasarawa a kawnakin baya.
Mata ‘yan asalin Cibok mazauna birnin Tarayya sunyi tururuwa zuwa Majalisar Kasa sanye da bakaken riguna, inda suka kai kukansu game ‘ya’yansu mata sama da 200 da aka sace a makarantar Sakandare dake Cibok.
Majalisar kasa ta ce Gwamnatin Tarraiyya ta samo yan matan nan da yan ta'adda suka sace ko suna da rai ko babu.
Mutanen garin Madagali, sun gudu sun bar gari, bayan hari dan 'yan bindigan da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kaimu a baya-bayannan.
Gwamnonin Jihohi biyu daga cikin ukun da aka sakawa dokar-ta-baci a arewa maso gabashin Najeriya sun soki lamirin dattijo Edwin Clark, wanda yayi kiran ciresu saboda lalacewar tsaro a yankin.
A wata fira da wakilin Muryar Amurka yayi da wani dan majalisa ya bayyana yadda dajin Sambisa yake wanda ko a tsakar rana ba'a iya shiga cikinsa ba tare da fitila ba.
A wani kokarin kawo karshen kashe-kashe tsakanin kabilun Tiv da Jukun da Fulani gwamnatin jihar Taraba ta kafa kwamitin zaman lafiya
Kowace ranar Allah takaicin iyayen dalibai matan da aka sace a Chibok sai karuwa ya ke yi saboda rashin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki da kuma jita-jita daban-daban da su ke ta ji.
Yau makonni uku kennan da sace dalibai mata su sama da dari biyu daga makarantarsu ta sakandare a garin Cibok dake jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya, a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe.
Yayin da aka share makonni uku da sace dalibai mata a makarantar Sakandare dake Cibok a Jihar Borno, wani dan Majalisar Wakilai ya tabbatar cewa 'yan bindigar sun fara auren 'yan matan.
Domin Kari