Hukumomin arewacin Najeriya sun ce har yanzu babu labarin 'yan mata 'yan makaranta dari biyu da saba'in da shida daga cikin wadanda aka sace a wata makaranta a watan jiya.
Babban darektan hukumar agajin gaggawa ta babban birnin tarayyar Najeriya, Abbas Garba Idris ya ce mutane 19 ne suka rasa rayukan su sanadiyar fashewar wata motar boma-bomai a tashar motocin safa da ke bayan garin babban birnin na Abuja.
A wani al'amari mai nuna dan'uwantaka tsakanin matasan kasa da kasa, a Sudan daliban Jami'a sun yi zanga-zangar neman a maido da dalibai matan da aka sace a garin Chibok na Jihar Borno
Gwamnatin jihar tTaraba ta musanta zargin cewa akwai sansanin 'yan kungiyar Boko Harama jihar.
A wani gangamin neman yancin arewa da aka shirya a Kano dattawan arewa da matasan sun kuduri aniyar yin aiki tare domin su kwato yankin daga kangin da ya shiga yanzu.
Yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane 19 a lokacin da bam na biyu ya tashi a daura da tashar motar Nyanya, a wajen birnin Abuja.
Mrs. Kema Chikwe wadda itace shugaban matan PDP ta kasa, ta bayanna shakkar sace daliban Cibok.
An dage karar da Manjo Al-Mustapha ya shigar game da zargin kazafin shirin kisan Gillar da Sheikh Sanusi Khalid Yayi Masa.
A dai-dai lokacin da za'a iya cewa jama'ar Najeriya sun fara kosawa da rashin tsaro da ya addabi wasu sassan kasar, abun dubawa anan shine, wani rawa gwamnati ya kamata ta taka game da tsaron mutanenta?
Gwamnan Jihar Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi bakoncin maza da mata masu neman Shugaban Kasa ya dauki matakin nemo dalibai mata da aka sace su sama da 200 a makarantar Sakarandaren Cibok dake Jihar Borno.
Daruruwan mata ne sukayi zanga-zangar lumana da maracen jiya a Kano dangane da abin da suka kira halin ko in kula da gwamnatin Tarayyar Najeriya ke yiwa batun ‘yan mata 234 da ‘yan bindiga suka sace a kwalejin ‘yan mata ta garin Chibok na jihar Borno fiye da makonni biyu da suka gabata.
Akwai rashin fahimta akan ko su waye Boko Haram, da kuma manufarsu a dai-dai lokacin da suke cigaba da tayar wa mutane hankula.
Domin Kari