WASHINGTON, DC —
Yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane 19 a lokacin da bam na biyu ya tashi a daura da tashar motar Nyanya, a wajen birnin Abuja, dab da inda aka kai wani mummunan harin bam da ya kashe mutane fiye da saba'in kimanin makonni biyun da suka shige.
Darekta janar na Hukumar Agajin gaggawa ta Babban Birnin Tarayya, Alhaji Abbas Idris, ya fadawa VOA Hausa cewa mutane kimanin 60 sun ji rauni, yayin da aka duba aka sallami wasu mutanen su 6.
Darekta janar din yace wannan bam ya tashi a cikin wata motar da aka je aka ajiye a karamar hanyar dake gefen babbar hanyar motar da ta shiga Abuja daga Keffi9, daidai tashar motar ta Nyanya.
Yace motoci guda 6 sun lalace.
A kasance da VOA Hausa domin jin bayanai na baya-bayan nan game da wannan harin bam na Nyanya.