Bayan da majalisar zartaswa ta kasa ko FEC ta kammala taronta ministan yada labarai Labaran Maku ya fito fili ya zargi 'yan jarida da 'yan adawa da zazzaba matsalolin tsaro a kasar.
Biyo bayan kwantar baunar da aka yiwa wasu sojoji har hudu suka rasa rayukansu a kauyen Gidan Bua dake Langtang Ta Kudu, yanzu hankula sun fara kwantawa.
Kwamishanan shari'a na jihar Boron ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatin jihar ta horas da 'yan gora wadanda aka fi sani da suna, Civilian JTF a takaice, horo.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, tace idan har Amurka ta san inda ake garkuwa dasu ba zata fada ba.
Maimakon yin bikin ranar yara ta duniya kamar yadda aka saba kowace shekara gwamnatin jihar Neja ta mayarda ranar ranar addu'o'i sabili da yaran da kungiyar Boko Haram ta rutsa da su da kuma 'yan mata fiye da dari biyu da take garkuwa da su.
Hanyar Abuja zuwa Nasarawa itace fitatciya da ta had duk jihohin dake arewa maso gabas har da Filato da Benue
Wasu 'Yan Najeriya na Korafin Akan Jawaban Shugaban Kasa a Coci.
Kimanin sojoji 24 da ‘yan sanda 21 ne suka rasa rayukansu, biyo bayan wani hari da ‘yan bindiga wadanda ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai a garin Yadin Buni dake Jihar Yobe, daya daga cikin jihohin dake da dokar ta baci a arewa maso gabashin Najeriya.
Daya daga cikin shuwagabannin Kungiyar Dattawan Chibok a Jihar Borno dake Najeriya, yace kwamitin da shugaban kasa ya kafa saboda daliban da aka sace ya gaza haduwa da kungiyar, da kuma kai ziyara Chibok duk da cewa kwamitin yayi alkawarin yin haka.
Wani babban jami'in sojin Nijeriya ya ce yanzu hukumar sojin kasar ta san inda masu kaifin kishin Islama su ke tsare da dalibai 'yan mata sama da 200 dinnan, to amma ya ce zai yi wuya a yi amfani da karfi wajen bukutar da su.
'yan kasuwar taminus dake garin Jos inda aka kai harin bamabamai makon da ya gabata sun bukaci gwamnati da ta hanzarta sake bude kasuwar
Ba'a za'a gudanar da bikin ranar yara na duniya ba wannan shekarar a jihar Neja domin irin bala'o'in da suka addabi dalibai a Buni Yadi inda wasu suka rasa rayukansu da Chibok inda aka sace wasu fiye da dari biyu.
Domin Kari