WASHINGTON, DC —
Gwamnatin jihar Neja tace ba zata gudanar da bikin ranar yara ba na wannan shekarar sabili da abubuwan da suka addabi yara a arewacin kasar.
Ranar yara ta duniya ana gudanarwa ne ranar 27 na watan Mayun kowace shekara. Gwamnatin jihar tace bikin na wannan shekarar ya zo ne daidai lokacin da Najeriya ke zaman makoki na sace yaran makarantar sakandare dake Chibok a jihar Borno da wasu 'yan bindiga suka yi da kuma kisan gillar da aka yiwa wasu yaran makarantar gwamnatin tarayya dake Buni Yadi cikin jihar Yobe.
Hajiya Hasana Adamu kwamishaniyar harkokin mata da walwalar jama'a ta jihar tace wannan ranar ba rana ba ce da zasu yi biki ba. Tace kasar bata cikin zaman lafiya. Koina mutum yake yana zaman dar-dar ne sanadiyar rashin sanin abun da ka faru kowane lokaci. Ban da haka an kashe yara a Buni Yadi an kuma sace wasu a Chibok. Sabili da haka ba za'a yi wani biki ba wannan shekara.
Maimakon bikin gwamnati ta shirya taron addu'o'i na addinin Musulunci da na Kirista. An gayyato malamai daga masallatai da mijami'u hade da wasu yara da zasu yi addu'o'in samun zaman lafiya a Najeriya.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.