Kungiyoyi masu yin fafitikan ceto daliban Chibok suna cigaba da yin zanga-zanga akan rashin amincewarsu da shirin gwamnatin tarayya domin ceto daliban.
Yayin da yake karbar malaman da suka yi zanga-zangar lumana domin nuna takaicinsu akan sace daliban Chibok gwamnan Sokoto Aliyu Magatakardan Wamako yace yanzu ba lokaci ba ne na dorawa kowa laifi.
Sojoji a garin Nsukka dake jihar Enugu yankin kudu maso gabas sun kafke wasu 'yansanda dauke da muggayen makamai akan hanyarsu ta zuwa arewa maso gabas.
Gibin dake tsakanin arewa da kudancin Najeriya akan ilimi ya kara fadi domin tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya inda yanzu kudancin kasar ya kara tserewa arewa
Wasu iyayen daliban da aka sace sun bi sawun 'ya'yansu har sun hangosu a karkashin bishiya amma sojoji sun kasa su rufa masu baya domin su kwato daliban kafin su yi nisa.
Maharin ya auna 'yan kallon kwallon kafa ne a wani wuri inda aka samar da talabijin domin masu sha'war kallon kwallon kafa.
Tosffin jami'an siyasa mata da wadanda suke kan gado sun yi taron karfafawa mata gwiwa su cigaba da karatunsu domin kada su bari abun da kungiyar Boko Haram tayi a Chibok ya karya masu gwiwa.
Kungiyar Boko Haram ta sake kai hari yankin Madagali cikin jihar Adamawa karo no hudu cikin wata guda inda ta haddasa asarar rayuka da dukiya
Karancin Wutar lantarki ya jawo koma baya ga harkoki n masana'atu a jihar Borno
Akwai hadin baki na wasu manyan sojojin a Boko Haram.
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ta amsa kukan Najeriya Alhamis dinnan, na sakawa Boko Haram takunkumi domin yanke hanyoyin samun kudadensu da makamai.
Domin Kari