A cikin firar da yayi da Muryar Amurka tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a jam'iyyar APC Dr. Haruna Yerima ya nuna shakku kan baiwa tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sheriff Kariya.
Mataimakin shugaban Najeriya Mohammed Namadi Sambo ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa Kano domin mika ta'aziyar gwamnati ga al'ummar Kano.
Jami’an tsaro, a Damaturu babban birnin jihar Yobe sun fatattaki, ‘yan bindiga, da ake zato 'yan kungiyar Boko Haram ne, da suka yiwa garin Damaturu.
‘Yan gwagwarmayan kwato ‘yan matan Chibok, a karshen mako ke kara kaimi ga kamfe din neman dawo da matan.
Arangamar tsakanin 'yansandan da jama'ar garin Jega ta biyo bayan wani farmaki da wasu 'yan fashi da makami suka kaiwa wani hamshakin dan kasuwa
Al'ummar Jama'atul Nasril Islam ko JNI tace wanna shi ne karon farko da za'a shiga masallaci a kai hari bayan an tayar da kabara a kashe mutane, lamarin da suka ce ya girgizasu.
Gwamnan Borno Kashim Shettima da Shehun Borno Garba El-Kanemi tare da wasu manyan mutanen jihar sun yi wata ganawar siri da tsohon shugaban Najeriya Janaral Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB a takaice.
Shugaban shugabannin samarin Najeriya Alhaji Sani Iro Daura, yace taron ya zama tilas ganin halin tsaro a kasar.
Janar Babangida mai ritaya yayi wannan kiran ne dangane da harin da akai a babban masallacin Kano.
Wata hukumar farar hula da ake cewa Civil Defense ta gano wani wurin da ake karkata akalar kayyakin agaji.
Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya lashi takobin cewa gwamnatinsa zata dauki dukkan matakan daya kamata domin farauto yan ta'adar da suka kai hari baban Masalacin Kano, suka kashe fiye da mutane tamanin da raunana akalla mutane dari.
Har yanzu hukumomi ba su bayyana adadin mutanen da suka mutu ko wadanda suka jikkata a hare-haren bama-bamai da aka kai a Babban Masallacin Jumma'a na Kano jiya ba.
Domin Kari