Ziyarar Firai Ministar Denmark Mette Frederiksen ita ce ta farko a Ghana. Wannan ziyarar ta karrama cika shekaru sittin da huldar diflomasiya tsakanin Denmark da Ghana ce. ‘Yan kasar Denmark na ganin kasar Ghana a matsayin muhimmiyar kawar kawance a Afrika ta yamma da baki dayan Afrika.
Wani bam da ya tashi a jiya Lahadi da rana a wajen babban masallacin birnin Kabul ya kashe akalla fararen hula biyar kana ya jikata akalla wasu mutane hudu, inji Qari Saeed Khosti, kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida na Taliban.
Kamar yadda aka zata tun farko, jawaban Shugabannin na Afurka sun fi raja'a ne ga batun annobar COVID-19, matsalolin tsaro da kuma na tattalin arziki.
Taron na wannan shekara ya banbanta da yadda aka saba gani a shekarun baya, inda dubban mutane ke halartar wannan taro dake tattaro shugabannin kasashe da firai ministoci da manyan tawagogi da kuma wakilai na kungiyoyi masu zaman kansu zuwa nan birnin New York.
Blinken ya kore duk sukar da ake yi wa hukumomin Washington cewa ba su kimtsa da kyau ba, duba da yadda rundunar dakarun Afghanistan ta durkushe cikin sauri.
Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani tare da mataimakinsa da kuma wasu manyan jami’an gwamnatin sa, sun bar kasar yau Lahadi, lamarin da ya bai wa mayakan Taliban dama su sake komawa kan mulki bayan shekara 20 da sojojin da Amurka ke wa jagoranci suka hambarar da su daga kan karagar mulki.
Sai dai Abdullah Abdullah, wanda shi ke jagorantar majalisar sasantawa a kasar, ya wallafa wani sakon bidiyo a Facebook, yana sukar Ghani.
Ma’aikatar harkokin wajen Indonesia ta bayyana nadamar ta bayan da jami’an shige da fice a Jakarta suka tsare wani babban jami’in diflomasiyya na Najeriya karfi da yaji, lamarin da ya sa gwamnati ta kira jakadanta da ke Abuja don tuntuba.
Ma’aikatar ayyukan hajji ta ba dukan mata izinin gudanar da ayyukan haji ta tare da Mehrem ba, idan zasu tafi cikin gungun ‘yan’uwansu mata.
Wasu ‘yan kasar Colombia da ‘yan sandan kasar Haiti suka tsare dangane da kisan gillar shugaban kasar Jovenel Moise sun halarci shirye-shirye na horo da karatu na sojojin Amurka, kamar yadda kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya tabbatar a cikin wata sanarwa da aka aikawa VOA.
Jami’ai a kasar Haiti sun fada daren jiya Alhamis cewa fiye da mutane 12 ne ke tsare dangane da kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar Haiti Jovenel Moise.
Shugaban 'yan sandan kasar Haiti ya ce an kashe mutane hudu da ake zargi da kisan shugaba Jovenel Moise jiya Laraba a wata musayar wuta da ‘yan sanda.
Domin Kari