Kasashen Afurka da dama ne suka yi jawabai jiya a wuni na uku na taron kolin Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a birnin New York. Galibinsu sun yi jawaban nasu ne a babban zauren taron Majalisar, kana wasu kuma daga ciki sun aiko da sakonnin jawabansu ne ta bidiyo.
Shugabannin Afurka da su ka yi jawaban sun hada da Cyril Ramaphosa, Shugaban Afurka Ta Kudu; Eric Keabetswe Masisi, Shugaban Botswan, João Manuel Gonçalves Lourenço, Shugaban Angola; Roch Marc Christian Kaboré, Shugaban Burkina Faso; Hage Geingob, Shugaban Namibia; Emmerson Dambudzo Mnangagwa, Shugaban Zimbabwe; Mahamat Idriss Déby Itno, Shugaban Chadi; Azali Assoumani, Shugaban Comoros; Ali Bongo Ondimba, shugaban Gabon.
Sauran Shugabannin Afurka da su ka yi jawabai a rana ta uku din Samia Suluhu Hassan, Shugabar kasar Tanzania wadda ita ce kadai shugabar kasa mace daga Afrika da ta yi jawabi. Akwai kuma Manneh Weah, Shugaban Liberia.
Shugaba Ramaphosa na Afrika ta kudu ya yi kira ga majalisar da ta bada dama ga kasashe su fara yin rigakafin COVID-19 musamman kasahen masu tasowa irin na Afurka. Ya yi takaicin rashin daidaito wurin raba rigakafi tsakanin kasashe a duniya. Yace wannan wani laifi ne ga bil Adama game da raba rigakafin COVID-19 a duniya, inda kasashe masu hannu da shuni suka saye sama da kashi 80 cikin 100 na rigakafin kana matalauta kuma aka bar su da kasa da kashi 1 cikin dari. Ya kara da cewa in ba mun magance wannan matsala cikin gaggawa ba annobar zata dade tare da mu, kana akwai yiwuwar sake ganin wata annobar.
Kowane shugaba na Afurka ya yi Magana a kan batun COVID-19 da kalubalen dake tattare da raba rigakafin cutar, wanda galibin kasashen basu da kudin saye.
Shima Roch Marc Christian Kaboré, Shugaban Burkina Faso ya tabo wannan magana amma kuma ya karkatar da jawabinsa a kan batun rashin tsaro a yankin Sahel, yana mai cewa “…A fannin yaki da ‘yan ta’adda kokarin kasashen dake fama da ayyukan ‘yan ta’addan zai yi tasiri mai dorewa ne idan suka samu taimakon kasashen duniya, ko shakka babu batun tsaro da zaman lafiyar yankin Sahel ba na kasashen yankin kadai ba ne, da suka hada da Burkina Faso, Mali, Mauritania, Nijer da kuma Chadi.
Shugaban gwamnatin soja na wucin gadi a kasar Chadi, Mahamat Idriss Déby Itmo, ya ce kasarsa tana bukatar tallafi wurin bunkasa tattalin arzikinta bayan nakasa ta da annobar COVID-19 ta yi. Deby wanda ya karanto jawabinsa ta hoton bidiyo, ya yi matashiya yana cewa “..A tuna cewa rashin tabbas da matasa ke ciki a yankin Sahel shine ke jefa su cikin tarkon akidar tsaurin ra’ayi; kana ya tura su bulaguro zuwa Turai, duk da irin hatsari dake tattare da tafiyar.
Akwai kuma kasashe kamar Iraqi, da Cuba, Macedonia ta Arewa, Guyana, Panama, Nauru da sauransu.
A yau ne kuma ake sa ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabinsa a babban zauren taron na MDD.
Ga Baba Yakubu Makeri da cikakken rahoton: