Mahukuntan kasar Haiti sun bayyana wata tawagar sojojin haya su 28 dauke da muggan makamai, wadanda suka hada da ‘yan kasar Kolombiya 26 da Amurkawa yan asalin kasar Haiti 2, wadanda ke da hannu a kisan Moise , mai shekaru 53, a gidansa na kashin kansa da ke unguwar masu hannu da shuni da ke wajen babban birnin kasar Port-au-Prince, kafin hudowar rana a ranar Laraba.
Shugaban ‘yan sanda Haiti, Leon Charles, ya fada jiya Alhamis cewa ana tsare da mutum 17, wadanda biyu Amurkawa ne da kuma 15 ‘yan Kolombiya.
Charles ya ce an kashe wadanda ake zargi mutum 3 kuma ana cigaba da neman 8. Tun da farko dai yan sanda sun ce an kashe wadanda ake zargi mutum 4. Sai dai Charles ko jami’an ‘yan sanda basu bayyan bambanci da ka samu ba.
Da safiyar yau Jumma’a, Taiwan ta fitar da wata sanarwa cewa, an kama wasu mutum 11 a harabar ofishin jakadancin ta a Port-au-Prince bayan da suka yi yunkurin tserewa ‘yan sanda.