Dakarun Rasha da ke kula da makamin nukiliya suna zaune cikin shiri bayan da Shugaba Vladimir Putin ya ba su umarni.
Wannan mataki da Rashar ta dauka na zuwa ne yayin da a ranar Litinin din nan Majalisar Dinkin Duniya take shirin yin wani zama na musamman kan yadda za a kara nuna matsin lamba ga hukumomin Moscow ta hanyar diflomosiyya kan mamaya da suka yi wa Ukraine.
A ranar Lahadi Putin ya fadawa Ministan tsaron kasar da ya umarci sojojin da ke kula da makaman nukiliya da su kimtsa saboda shugabannin NATO na furta wasu “kalamai masu zafi” tare da saka takunkumin karya tattalin arzikin Rasha saboda ta mamaye Ukraine.
Sai dai yayin wani zama da aka yi na musamman a Majalisar Dinkin Duniyar, Jakadar Amurka Linda Thomas Greenfiled, ta ce Rasha “ba ta fuskantar wata barazana daga NATO,” kuma dakarun gamayyar ba za su yi fada a Ukraine ba.
Wani babban jami’in tsaron Amurka ya fadawa manema labarai cewa, matakin da Rashar ta dauka na kimtsa makamanta na nukiliya “bai taso ba” kuma hakan zai kara “rura wutar,” rikicin ne.
- Wannan rahoto ne da Carla Babb da Scott Stearns suka rubuta wanda Mahmud Lalo ya fassara.