Hukumar ‘yan sandan Ghana ta zargi jakadar Burtaniya a Ghana, Harriet Thompson, da shiga harkar da ba ta shafe ta ba, biyo bayan rubutun da ta yi a kan shafinta na Twita da take bayyana ra’ayinta a kan sake kama mai fafutukar ‘#Fixthe Country’ da aka yi, a hanyarsa ta zuwa kotu.