Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Girgizar Kasa Ta Halaka Daruruwan Mutane A Afghanistan


Wani gida da girgizar kasa ta daidaita a Afghanistan
Wani gida da girgizar kasa ta daidaita a Afghanistan

Hukumomin Taliban sun ce a ranar Laraba girgizar kasa ta kashe fiye da mutum 900 tare da jikkata wasu akalla 600 a kudu maso gabashin kasar.

Mataimakin ministan kula da ayyukan agaji na Taliban Mawlawi Sharafuddin Muslim ne ya bayyana adadin wadanda suka mutu a wani taron manema labarai a Kabul babban birnin kasar, a lokacin da yake ba da bayanan farko.

Ya kara da cewa akasarin barnar ta faru ne a Lardunan kudu maso gabashin Pakistan da Khost da ke kan iyaka da Pakistan.

Masu ba da agajin gaggawa bayan aukuwar girgizar kasar
Masu ba da agajin gaggawa bayan aukuwar girgizar kasar

Hukumar binciken yanayin kasa (USGS) ta Amurka ta bayyana cewa girgizar kasar mai karfin maki 6.1 ta auku ne da sanyin safiyar Larabar.

Bidiyon da aka yi ta yadawa a kafafen sada zumunta sun nuna yadda girgizar ta yi daidai da gidaje da baruguzai.

Har ila yau an ji hucin girgizar kasar a Kabul, babban birnin kasar ta Afghanistan

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG