Kasar Qatar ta kaddamar da bincike kan mutuwar wani dan kasar Philippines biyo bayan rahotannin da ke cewa, mutumin ya mutu ne a wani wurin horo a lokacin gasar cin kofin duniya.
Masu gabatar da kara a Jamus sun ce wasu jami’ai dubu 3,000 ne suka gudanar da bincike a wurare 130 a jihohi 11.
Shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru kuma tsohon dan wasan kwallon kafa Samuel Eto’o ya nemi afuwar wani mutum da ya ture kasa a wani abin da ya kira ‘mummunar hatsaniya’ a wajen wani filin wasa na gasar cin kofin duniya da safiyar Talata.
Shugaban kasar Nijar ya nemi a samar da yarjejeniyar daukar ma’aikata daga kasashen Afirka zuwa Turai, don magance matsalar kwararar bakin zuwa Turai
Jakadan Najeriya a kasar Rasha, Farfesa Abdullahi Yibaikwal Shehu, ya ja hankalin sabbin daliban Najeriya da suka iso kasar Rasha a bisa tsarin tallafin karatu tsakanin Najeriya da kasar Rasha na shekarar 2022 zuwa 2023.
Yarima William na masarautar Burtaniyya da matarsa Kate sun tashi zuwa Amurka a ranar Laraba don kai ziyara a karon farko cikin shekaru takwas.
Babban jigon darikar Katolika Cardinal Richard Kuuia Baawobr kuma shugaban majalisan limaman darikar katolika a nahiyar Afrika, ya rasu a jiya a birnin Roma na kasar Italiya.
Saudiyya ta samu gagarumar nasara yau Talata bayan da ta doke Argentina da ci 2-1 a wasansu na farko a gasar cin kofin duniya ta maza a Qatar.
Daraktan Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI, Christopher Wray, ya ce Hukumar FBI na gudanar da bincike kan gudanar da “ofishin ‘yan sanda” ba bisa ka’ida ba da kasar China ke yi a New York na Amurka.
Bayanan Babban Bankin Najeriya na nuni da cewa, an kashe sama da Naira biliyan uku da rabi kan harkokin ilimi a kasashen ketare tun daga shekarar 2015 da gwamnatin Muhammadu Buhari ta hau kan karagar Mulki zuwa wannan shekara da muke ciki ta 2022.
An gunadar da bukin yaki da ciwon suga da kuma ake kira ciwon sukari na Hukumar lafiya ta duniya bana da taken 'Samun ilimi game da ciwon sukari don kariya. '
Wani babban jirgin ruwa na jigilar mai da hukumomin Najeriya ke zarginsa da yunkurin lodin danyen mai ba bisa ka'ida ba, na kan hanyarsa ta komawa kasar, kamar yadda kakakin rundunar sojin ruwan Najeriya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Juma'a.
Domin Kari