Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kashe Dala Biliyan 3.5 Wajen Biyan Kudin Makarantar Dalibai A Kasashen Waje


Daliba a kasar waje
Daliba a kasar waje

Bayanan Babban Bankin Najeriya na nuni da cewa, an kashe sama da Naira biliyan uku da rabi kan harkokin ilimi a kasashen ketare tun daga shekarar 2015 da gwamnatin Muhammadu Buhari ta hau kan karagar Mulki zuwa wannan shekara da muke ciki ta 2022.

Bayan wannan kudade da gwamnatin ta kashe, su kansu yan kasar sun kashe biliyoyin daloli wajen biyan kudin makaranta a kasashen waje, ba tare da samun ribar wannan kudi ba na zahiri a cikin gida ba.

Irin wannan kudi dai da yan Najeriyan ke kashewa a kasashen wajen na kara karya darajar Naira akan kudin dala, inji masana tattalin arziki, wadanda suka ce kasar na fama da karancin dalar Amurka a asusunta na ketare.

Dalibi a kasar waje
Dalibi a kasar waje

Bayan wannan kuma, yawaitar yajin aikin malaman jami’o’i da na kwalejojin kimiyya da fasaha a kasar sun taimaka wajen sanya iyaye da dalibai kwadayin zuwa kasashen waje domin kammala karatun su na gaba da sakandare.

A kwanan nan ne dai kungiyar malaman jami’o’in kasar suka janye yajin aikin da suka shafe watanni fiye da 8 suna yi tare da neman gwamnati ta karawa makarantun kasar kudaden gudanarwa tare da samar da kayan aiki da kuma inganta rayuwar malamai da dalibai.

XS
SM
MD
LG