‘Yan sandan Mexico sun tsare wani likita da ake zargi da amfani da gurbataccen magani da ake zaton ya haddasa barkewar wani nau’in cutar sankarau a jihar Durango dake arewacin kasar.
Hankalin duniya ya karkata ga kai dauki Turkiyya da Siriya, inda mutane sama da 5,000 su ka rasu sanadiyyar girgizar kasa.
Da safiyar yau litinin wata Girgizar kasa mai karfin 7.8 a ma'auni ta kashe mutane sama da 2, 300 a kasashen Turkiyya da arewacin Siriya, yayinda aka fara aikin nemo masu rai a cikin baraguzan gine-gine da suka rubta.
Sojojin Amurka sun ce sun kakkabo wannan baban bala-balan din kasar China na leken asiri a yankin gabar tekun Carolina.
Fafaroma Francis ya je Afirka ta tsakiya yau Talata domin kai sakon zaman lafiya ga kasashe biyu da ke fama da tashe-tashen hankula a yankin.
Wani tashin bam mai matukar karfi, ya tarwatsa wani masallaci mai cinkushe da mutane a Arewa maso yammacin Pakistan a yau dinnan Litini, ya hallaka masu ibada a kalla 59, ya kuma raunata wasu sama da 150.
Manyan jami'an kasashen China, Rasha, da kuma Amurka suna kokarin ziyartar kasashen Afirka a wannan watan don yin alkawarin ba da gudummuwa ga nahiyar da ke bunkasa cikin sauri a duniya.
Ana ci gaba da cece kuce a yanar gizo game da amincewar biyan tarar da jami’an yan sandan garin Lancashire suka kakabawa Fira Ministan Birtaniya, bayan da asirinsa ya tonu a hoton kafar sadarwa na Instagram.
Yau Laraba wani jirgin sama mai saukar ungulu a wajen babban birnin kasar Ukraine, ya kashe mutane akalla 15, ciki har da ministan harkokin cikin gida Denys Monastyrsky.
“Ina mai alhinin sanar da ku rasuwar mataimakina, mai girma Badara Alieu Joof.” Barrow ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Sabon faifan bidiyo da ke daukar hankulan miliyoyin masu amfani da shafukan sada zumunta na wani yaro dan kasar Jamaica mai shekaru 10 yana waka kan kyau da godiya, ya gama duniya.
Kasar Nepal na gudanar da zaman makoki a yau Litinin, kwana guda bayan da jirgin saman Yeti Airlines ya yi hatsari dauke da fasinjoji 72 da ma'aikatan jirgin daga Katmandu zuwa garin Pokhara na masu yawon bude ido.
Domin Kari