Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkalan Turai Sun Takawa Birtaniya Birki Kan Karkatar Da Bakin Haure Zuwa Rwanda


Wasu Bakin Haure Da Yan Sanda Suka Kama A Birtaniya.
Wasu Bakin Haure Da Yan Sanda Suka Kama A Birtaniya.

Birtaniya ta yi kira da a yi wa kotun Turai garambawul, bayan da alkalan da ke can suka hana zirga-zirgar jiragen da ke dauke da masu neman mafaka zuwa kasar Rwanda domin a tantance su a can.

An samu karuwar kwararar bakin hauren da ke isa cikin kananan kwale-kwale a gabar tekun Birtaniya, kuma gwamnati ta yi imanin cewa manufar tura su Rwanda, ita ce za ta hana mutane da damar yin wannan balaguron mai hatsari.

Sai dai kamar yadda Henry Ridgwell ya ruwaito, manazarta da dama sun ce kawayen Birtaniya na Turai ba su da sha'awar sake fasalin kotun.

Hukumomin Birtaniya sun gano bakin haure kusan dubu bakwai da ke tsallakawa teku cikin kananan kwale-kwale daga Faransa ya zuwa wannan shekara. Jimlar a shekarar 2022 ta wuce 45,000. Firayim Ministan Burtaniya Rishi Sunak cikin kalamansa ya sha yin alkawarin "dakatar da jiragen ruwan."

Don haka Birtaniya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Kigali a shekarar da ta gabata, wadda ba za ta karbi yawan bakin haure da ba a bayyana adadinsu ba, domin a tantancesu a can, tare da basu mafaka a kuma sake tsugunar da su – ba tare da izinin daukaka kara ba. Tuni dai Birtaniya ta biya Rwanda dala miliyan 150 a karkashin yarjejeniyar.

Amma alkalai a Kotun Kare Hakkin Bil Adama ta Turai ba su yarda ba. A dai dai lokacin da jirgin farko ke shirin tashi zuwa kasar Rwanda a watan Yunin da ya gabata, kotun ta fitar da abin da aka fi sani da umurnin "Dokar 39" toshe zirga-zirgar jiragen sama a kan dalilin cewa watakila sun keta yarjejeniyar Majalisar Turai kan 'Yan cin Dan Adam, wacce Birtaniyya ta rattaba hannu. Majalisar Turai ba ta cikin Tarayyar Turai.

A martanin da gwamnatin Birtaniya ta mayar, ta bullo da wasu sabbin dokoki da za su yi watsi da hukuncin kotunan Turai. Yanzu haka dai ana muhawara kan kudirin dokar a majalisar dokokin kasar.

Kuma a wani taro na Majalisar Turai a wannan makon, Firayim Minista Sunak, ya ce zai yi kokarin shawo kan abokan huldar Turai su yi wa kotun da kanta kwaskwarima.

Sama da kashi daya bisa hudu na bakin hauren da suka isa kan kananan kwale-kwale a shekarar 2022, 'yan kasar Albaniya ne.

Birtaniya ta kori sama da dubu daya zuwa kasarsu. Firayim Ministan Albaniya, ya fada a watan da ya gabata cewa Birtaniyya tana cikin wani hali saboda gudun hijira.

XS
SM
MD
LG