Birnin Makka mai daraja ya karbi bakunci dubban mutane daga kasashe dabam-daban na fadin duniya don gudanar da aikin Hajjin bana na hijira ta 1444, wanda yayi daidai da shekarar 2023 miladiyya.
Alhazan duniya kimanin milIyan biyu ciki har da 'yan Najeriya ne ke shirin hawan Arafah a ranar Talata, yayin da wasu ‘yan Najeriya ke da burin yi wa kasar addu’ar zaman lafiya.
Hukumar Alhazan Najeriya ta Kammala Jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa Saudi Arabiya a ranar Asabar 24 ga wannan wata, kwana uku kafin hawan Arafat.
A yayin da yake bitar karshen aiyukan jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki a albarkacin hajin shekarar 1444 da ke dai dai da shekarar mai ladiya ta 2023 shugaban hukumar alhazzan Nijer Commissaire Ibrahim Kaigama, ya tabbatar da cewa an yi nasarar isar da dukkan maniyatan kasar a kan lokaci.
Halartar shugaba Tinubu a wannan taro na nuni da kokarin Najeriya wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa da kuma neman habaka tattalin arzikinta.
Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fama da matsalolin rayuwa, wasu gwamnatoci sun himmantu wajen kara lalabo hanyoyin saukaka halin matsi da jama'ar su suke ciki.
Birtaniya ta sanar da cewa a shirye take ta rage haraji da take daurawa akan kayayyakin da ake shigo da su daga Nigeriya da wasu kasashe masu tasowa.
Jami’an Hukumomin Alhazai sun garzaya zuwa Mina, Arfa da Muzdalifa don tabbatar da komai na tafiya daidai gabanin fara aikin Hajjin nan da sati guda.
Majalisar Dattawa ta tabbatar da Nusrat Chowdhury, wata lauya mai kare hakkin jama'a, a matsayin Musulma ta farko da ta zama alkalin tarayya a tarihin Amurka.
Bayan shafe wata 9 da rattaba hannu a kan yarjejeniyar bututun iskar gas tsakanin Kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPCL da gwamnatin kasar Morocco, an sami karin kasashe 11 da suka shiga sahun kasashen 2.
Jami’ai a kasar Canada sun ce akalla mutane 15 su ka mutu a ranar Alhamis a lokacin da wata babbar motar daukar kaya ta yi karo da wata karamar motar safa da ke dauke da wasu mutane, galibi dattawa, a kan hanyarsu ta zuwa gidan caca a lardin Monitoba na kasar Canada.
Jami'an kiwon lafiya na Falasdinu sun fada ranar Alhamis cewa sojojin Isra'ila sun harbe wani Bafalasdine a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye.
Domin Kari