A ranar Talata ne Jakadan Saudiyya a Iran ya isa kasar daular Musulunci ta Iran, yayinda shima takwaran shi ya isa birnin Riyadh, lamarin da ya dinke maido da danganataka tsakanin kasashen yankin kogin Pashan biyu, bayan shafe shekaru bakwai da rushewar hulda tsakanin su.