Dokar ta rage shekarun mallakar fasfon daga takwas zuwa biyar.
Kungiyar ta Houthi ta ce suna nuna goyon bayansu ga Falasdinawa ne a daidai lokacin yakin da Isra'ila ke yi da mayakan Hamas a Gaza kuma sun kai hare-hare fiye da 30 a tekun Bahar Rum.
Solangi ya ce manufar taron ita ce yin nazari mai zurfi kan harkokin tsaron kasa bayan abubuwan da suka faru a Iran da Pakistan.
An shiga rana ta biyu ta tarzomar da ta tashi a tsibirin Comoros da ke tsakiyar tekun Indiya a yau Alhamis wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu akalla shida, in ji wani jami’in lafiya.
Masu aikin ceto sun kwaso gawarwaki bakwai daga cikin laka, ciki har da na yara. Wasu mutane hudu kuma har yanzu ba a gansu ba, Rocris Idul ya shaida wa AFP.
Wani rahoton da kamfinin dillancin labarai na Reuters ya wallafa a yau ya yi nuni da cewa, wani bincike da wasu fitattun masana tattalin arziki su ka fitar a yau Litinin ya gano cewa, a bana, tattalin arzikin duniya zai murmure a hankali.
Afirka ta Kudu ta ce fiye da kasashe 50 ne suka nuna goyon bayansu ga shari'ar da ta gabatar a babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya da ke zargin Isra'ila da kisan kare dangi a kan Falasdinawa a yakin Gaza.
Sojojin Amurka da na Birtaniyya sun yi ruwan bama-bamai kan 'yan Houthis da ke samun goyon bayan Iran a Yemen a ranar Alhamis, a wani gagarumin harin ramuwar gayya ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen yaki na Tomahawk da jirgin ruwan yaki da na karkashin ruwa, in ji jami'an Amurka.
Alkalai a Kotun Kasa da Kasa, sun fara sauraron ba’asi na tsawon kwanaki biyu daga yau Alhamis, a wata karar da kasar Afirka Ta Kudu ta shigar, ta tuhumar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a yakin da ta ke yi a Gaza.
Jami’ai a Pakistan sun haifar da cikas ga hawa yanar gizo da toshe kafar shafukan sadarwar zamani a kasar baki daya a yammacin jiya Lahadi.
‘Yan sandan Isra’ila sun bude wuta kan wasu da aka zarga da afkawa da mota kan wani shingen binciken ababen hawa a yammacin kogin Jordan, tare da mummunan harbin wata kamar yarinya Bafalasdina dake cikin wata mota dake hannun riga da motar, a cewar ‘yan sanda da jami’an kiwon lafiya.
Ma’aikatar Lafiyar ta ce harin na Isra’ila, ya auku ne a Khan Younis, wanda ke kudancin Gaza, kuma cikin wadanda su ka mutu din har da yara tara.
Domin Kari