Wani jirgin saman yakin Isra'ila mara matuki ya kai hari kan ofisoshin Hamas da ke yankin Beirut a daren jiya Talata, inda ya kashe babban jami'in Hamas Saleh al-Arouri, kamar yadda kungiyar mayakan da kafar yada labaran Mideast suka bayyana.
An caka wa shugaban jam'iyyar adawa ta Democratic a Koriya ta Kudu wuka a wuya, yayin wata ziyara da ya kai birnin Busan da ke kudancin kasar yau Talata, aka kuma dauke shi a jirgin sama zuwa wani asibitin Jami’a domin yi mashi jinya bisa ga cewar Jami'an jam'iyyar da na kashe gobara.
Yayin da agogon ya kai karfe 12 na dare a Australia, an saki abubuwan fashewa har tsawon minti 12 akan gadar Sydney Harbor da jama’a suka taru akai. don marabtar sabuwar shekara ta 2024.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya fada a jiya juma’a cewa Ukraine tana yakin ceton rai, bayan da Rasha ta kai gagaruman farmaki a fadin Ukraine.
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da barin wuta a Gaza babu kakkautawa, inda ta kai harin bama bamai da tanka a kan garin Khan Younis. Rahotanni sun ce wannan fatattakar na zuwa ne gabanin yanda ake zaton zai faru tun farko a cikin garin.
A makon da ya gabata jihar Colorado ta dauki irin wannan mataki na hana Trump tsayawa takara a zaben fitar da gwani a jihar.
Masar ta ba da tabbaci a ranar Alhamis cewa ta bullo da wani tsari da zai iya kawo karshen rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas a Zirin Gaza wanda ya kunshi matakai uku da za su kai ga cimma matsayar dakatar da bude wuta, tana mai cewa yanzu tana jiran a ba ta amsa kan wannan bukata da ta mika.
Akalla mutane 40 ne suka mutu sakamakon fashewar wata tankar iskar gas a Arewa ta tsakiyar kasar Laberiya, a cewar babban jami'in kula da lafiya na kasar ta yammacin Afirka, Francis Kateh, a ranar Laraba.
Alexander Novak, wanda ke kula da sashen makamashi na Rasha ya ce, "Babban abokan hulda a halin da ake ciki yanzu su ne China, wadda kasonta ya karu da kusan kashi 45% zuwa 50%, sai kuma Indiya."
A ranar Talata Majalisar Dinkin Duniya ta nada jami'ar da za ta sa ido kan jigilar kayayyakin jin kai zuwa zirin Gaza, a wani bangare na kudirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince da shi a ranar Juma'ar da ta gabata don bunkasa ayukan jin kai.
Shugaban kasar Belarus ya ce Rasha ta kammala jigilar makaman nukiliya da take yi zuwa kasarsa, matakin da ya haifar da kakkausar suka a makwabciyarta Poland da sauran kasashen yankin.
A lokacin manyan bukukuwa kamar Kirsimeti, 'Yan Afrika mazauna kasashen Turai sukan yi kewar gida, sakamakon sabbanin yadda ake gudanar da bikin.
Domin Kari