Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, Turkiyya na tsaye tsayin-daka da kasar Labanon a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saka tsakaninta da Isra'ila, ya kuma yi kira ga kasashen yankin da su marawa Beirut baya.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta samu wani shugaban masu tsattsauran ra'ayin Islama mai alaka da al-Qaida da laifin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Timbuktu na kasar Mali.
Shugaban Amurka Joe Biden ya fada cikin wata sanarwa cewa, al’ummar Haiti sun cancanci zama lafiya a gidajen su, su gina ingantacciyar rayuwa ga iyalan su, su kuma more yancin demokradiyya
Mutumin da ya kafa WikiLeaks Julian Assange zai amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a wata yarjejeniya da ma’aikatar shari’a ta Amurka, da za ta sa ya kauce tafiya gidan yari, da kuma kawo karshen yiwuwar wata doguwar shari'a da ta ta’allaka kan buga wasu tarin takardu na sirri.
Yankin Dagestan da ke kudancin kasar Rasha ya gudanar da zaman makoki na kwanaki uku a yau Litinin bayan wani harin da mayakan Islama suka kai inda suka kashe mutane 19.
Wasu fashe-fashe sun yi sanadin tashin gobara a wata masana'anta ta batirin lithium a Koriya ta Kudu a ranar Litinin, inda suka kashe ma'aikata 22, mafi yawansu 'yan kasar China, yayin da kamfanin ya kone kurmus.
Wadansu ma’aurata daga Bowie, jihar Maryland na daga cikin sama da mutane dubu daya da suka rasu sakamakon matsanancin zafi yayin aikin hajjin bana a kasar Saudiya.
Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fadi cewa dakarun kasarsa sun kusa kawo karshen "lokacin zafafa kai hare hare kan mayakan Hamas a Gaza na ba da jimawa ba.
Kasar Argentina mai rike da kofin ta lallasa Canada da ci 2-0 a wasan farko na gasar cin kofin Copa America da aka buga a Atlanta na jihar Georgia da ke Amurka a ranar Alhamis.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Gaborone ya fitar da wata sanarwa inda ya ce Amurka za ta dauki nauyin shirya wani taro da zai tattaro manyan jami'an tsaro na kasashen Afirka a Botswana A mako mai zuwa
Jami'an Amurka sun ce suna aiki ta hanyar diflomasiyya don ganin an kawar da barkewar mummunan fada tsakanin Isra'ila da mayakan Hezbollah masu samun goyon bayan Iran da ke kudancin Lebanon.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wasu jerin yarjeniyoyi da takwaransa na kasar Vietnam To Lam a yau Alhamis, yayin wata ziyarar aiki da ya kai kasar a daidai lokacin da Moscow ke neman karfafa alaka a nahiyar Asiya.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.