A cikin ‘yan wasa 60 da aka zabo a gasar NBA, akalla takwas suna da asali daga Najeriya. Ga kuma yadda aka zabe su. ‘Yan wasa sittin ne aka zaba a zagayen farko na gasar kwallon kwando ta NBA. Takwas daga cikinsu suna da asali sosia daga Najeriya.
Hukumar kwallon Kwando ta NBA a Amurka ta gudanar bikin tantance ‘yan wasan da za su buga wasanni a gasar ta NBA, wanda aka gudanar da shi ta kafar yanar gizo a garin Bristol da ke jihar Connecticut.
Najeriya na ganin dishi-dishi a kokarin da take yi na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a badi.
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa-da-kasa ya ce kwamitin zai dauki matakai don tabbatar da cewa an ba dukkan 'yan wasa da wadanda zasu halarci gasar wasannin riga kafin COVID-19 a watan Yulin shekarar 2021.
Rahotanni daga kasar Masar na cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Mohammed Salah ya kamu da cutar COVID-19.
Tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Diego Maradona na murmurewa cikin sauri bayan tiyatar da aka yi masa a kwakwalwa.
A karshen mako hukumar wasannin Kwando ta NBA ta tabbatar da cewa za ta soma wasanni kafin karshen shekara. Hukumar ta ce wasannin zasu fara ne daga ranar 22 ga watan Disamba.
Kocin tawagar kwallon kafar Ghana, C.K. Akonnor, ya fitar da jerin sunayen 'yan wasa 23 da za su yi wasan cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Afrika da kasar Sudan.
Dan wasan Super Eagles da ya taka rawar gani a wasannin shiga gasar cin kofin Afrika, Victor Osimeh, shi ne na farko a jerin sunayen ‘yan wasa da kocin Najeriya Gernot Rohr ya gayyace su domin karawa da Sierra Leon a wasan cancantar shiga gasar cin kofin Afirka.
Hukumar kula da harkokin kwallon kafar Afirka, CAF, ta tabbatar da cewar shugaban hukumar Ahmad Ahmad ya kamu da cutar COVID-19.
Daya da cikin manyan kungiyoyin Firimiya lig din Ghana, wacce ta taba lashe kofin zakarun Afrika, Accra Hearts of Oak, mai lakabin “Phobia” ta sanar da nadin wani dan kasar Portugal Carlos Manuel Vaz Pinto a matsayin sabon kocin kungiyar.
Akwai yiwuwar shugaban hukumar kwallon kafar Afrika ta CAF Ahmad ka iya samun wa’adi na biyu, na jagorancin hukumar, yayin da kasashe 46 cikin 54 mambobin hukumar suka bukaci ya sake tsayawa takarar shugabancin hukumar.
Domin Kari