An zabi ‘yan wasa 13 daga kasashe 10, bakwai daga cikin su a zagayen farko shida kuma a zagaye na biyu.
Kungiyar Miami Heat ta zabi Precious Achiuwa a matsayi na 20 sannan Utah ta zabi Udoka Azubuike a matsayi na 27.
Wannan shi ne karon farko da aka taba zabar ‘yan Najeriya biyu a zagayen farko na tantance ‘yan wasan da za su shiga yin wasa a gasar ta NBA.
Achiuwa da Azubuike na daga cikin mutum takwas da aka zaba da suka fito daga Najeriya ko kuma suke da mahaifi ko mahaifiya daga kasar.
“Da farko ina godiya ga Allah, ina godiya ga Allah da ya sa ni a wannan matsayi inda zan buga was aga babbar kungiya, wanda hakan zai b ani damar wakiltar kaina da kuma inda na fito.” In ji Achiuwa
Sauran sun hada da Isaac Okoro wanda kungiyar Cleveland Cavaliers ta zaba a matsayi na 5, sai Onyeka Okongwu wanda Atlanta Hawks ta zaba a matsayi na 6 yayin da Denver Nuggets ta zabi Zeke Nnaji a matsayin na 22.
“Dadi a ce kai ne dan Najeriya na farko da aka zaba. Kuma albarka ne, mahaifiyata ta kan yawan fada min cewa na tabbata na ci gaba da alfaharin ni dan Najeriya ne.” In ji Isaac Okoro.
Sauran sun hada da Daniel Oturu wanda Minnesota Timberwolves ta zaba a matsayi na 33 da Jordan Nwora wanda kungiyar Milawauke Bucks ta zaba a matsayin na 45.
Sannan akwai Desmond Bane da Boston Celtics ta zaba a matsayi na 30.
Kungiyar Minnesota Timberwolves ce ta fara zabar dan wasan, wannan kuma shi ne karo na biyu a tarihin wannan taro da take samun wannan damar, inda yta zabi Anthony Edwards na Georgia.
Kungiyar Golden State Wolves ce ta yi zabi na biyu inda ta dauki James Wiseman na Memphis.
Wannan zaman a tantance ‘yan wasan ya kai ga kasashe da yankuna 215 da masoya kwallon kwando suke sannan ya gudana cikin harsuna 29.