Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFCON: An Tashi Canjaras a Wasan Najeriya, Saliyo


'Yan wasan Najeriya.
'Yan wasan Najeriya.

Najeriya na ganin dishi-dishi a kokarin da take yi na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a badi.

A ci gaba da neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ‘yan wasan Najeriya Super Eagles sun tashi canjaras da takwarorinsu na kasar Saliyo a karawar da suka yi filin was ana Stevens da ke birnin Freetown a yau Talata.

A karawar da bangarorin biyu suka yi a ranar Juma’ar da ta gabata a birnin Benin, Saliyo ta yi nasarar tafiya da maki bayan da suka tashi kunnen doki 4-4.

Masu fashi baki da dama sun kalli wasan na Freetown a matsayin wanda ya zama jazaman Najeriya ta lashe, amma abin ya cutura.
A wasanta na gaba, Najeriya wacce ta taba lashe kofin gasar har sau uku, za ta kara da kasar Lesotho wacce ta taba dokewa da ci 4-2 a watan Nuwambar 2019.

Bayan da suka buga wasa hudu, ‘yan wansan na Super Eagles na ci gaba da zama a saman teburinsu na “L” da maki 8, sai Benin mai maki 7, Saliyo na da maki 3 yayin da Lesotho ke da maki 2 a kokarin shiga gasar ta AFCON wacce za a yi badi.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG